✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sandan Legas da Ogun sun tasar wa tsagerun Neja-Delta

A ƙarshen makon jiya ne wasu gaggan ’yan ta’adda da ake kyautata zaton tsagerun Neja-Delta ne da suka shigo jihohin Lagas da Ogun ta hanyoyin…

A ƙarshen makon jiya ne wasu gaggan ’yan ta’adda da ake kyautata zaton tsagerun Neja-Delta ne da suka shigo jihohin Lagas da Ogun ta hanyoyin ruwa suka yi kwantan ɓauna a yankunan Owutu da Ikorodu a Jihar Legas, yankunan da suke daura da Jihar Ogun a yankin garin Shagamu.
Tun da fari dai an yi ta yaɗa jita-jitar cewa tsagerun sun hallaka fiye da mutum 50 a ɓarin wutar da suka yi a yankunan, batun da Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas Fatai Owoseni ya ƙaryata, a zantawarsa da manema labarai; inda ya ce mutum 6 ne suka rasa ransu a hare-haren tsagerun. Ya ce ko a lokacin farmakin, babban  jami’in rundunar ’yan sandan da ke kula da yankin Owutu da jami’an ’yan sandan da ke yankin sun kai ɗauki kuma a yanzu rundunar ta jibge jami’anta na musanmman a yankunan domin jiran ko ta kwana.
Kwamishinan, wanda ya halarci wuraren da harin ya rutsa da su jim kaɗan da kai hare-haren, ya bayyana cewa iyalan mutum biyun da harin ya rutsa da su sun buƙaci a ba su gawarwakinsu, don yi musu sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Yayin da ragowar gawarwaki hudu aka kai su wajen adana gawa.
A Jihar Ogun mai maƙwabtaka da Legas ma jami’an ’yan sandan sun yi shirin ko ta kwana domin rundunar ta jibge tawagar dakarunta hudu, waɗanda suka haɗa da rukunin ’yan sanda na musanman masu yaƙi da ’yan fashi da makami da manyan laifuka a ƙarkashin jagorancin babban jami’in ’yan sandan da ke lura da garin Shagamu, Ali Janga.
A cewar Mataimakin Kwamishinan ’yan sandan jihar, a fannin aikace-aikace, Bello Makwashi, rundunar ta kai ga ɗaukar wannan matakin bayan shawarwari da bayanan da ta tattara. Ya ce Ali Janga zai ci gaba da sanya idanu a ayyukan tabbatar da tsaro na mussanma a yakunan da lamarin ya shafa, waɗanda suka haɗa da Elepete da Imuti da Kajola tare da Magbon da Ajegunle.
Bello Makwashi wanda ya yi magana da yawun Kwamishinan ’yan sandan jihar Abdulmajid Ali, ya shaida cewa an wadata jami’an ’yan sandan da duk makaman da ya kamata da kayyayakin aiki kana ya yi kira ga mazauna ’yankin waɗanda suka kaura cewa da su koma muhallansu don ci gaba da gudanar da harkokinsu, domin a yanzu an shawo kan lamarin.