✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

”Yan sandan Jigawa sun gano mutum 66 da suka mallaki bindigogi ba izini

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta samu nasarar kwato makamai daga ’yan fashi da mutanen da suka mallaki bindigogi ba bisa ka’ida ba, inda ta…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta samu nasarar kwato makamai daga ’yan fashi da mutanen da suka mallaki bindigogi ba bisa ka’ida ba, inda ta ce ta ce ta gano mutum su 66 da suka mallaki bindigogi ba tare da izini ba.

Kwamashinan ’Yan sandan Jihar Jigawa, Bala Zama Senchi ya ce sun kama bindigogi kirar gargajiya da na zamani guda 119 da ake yin farauta da su. Sauran bindigogi kirar zamani akwai Ak47 guda uku da AK56 guda biyu da wasu bindigogi kirar gida guda uku da karamar fistol irin ta ’yan sanda.

Sauran sun hada da bindiga kirar Nature da ake kira Pump Action guda daya da wasu kananan fistol-fistol kirar gida guda biyar. Kwamashinan ’Yan sandan ya ce wannan ya biyo bayan umarnin da rundunar ta kasa ta ba su ne na cewa duk wadanda suka mallaki bindigogi ba bisa ka’ida ba su mika su ga ’yan sanda cikin gaggawa.

Ya kara da cewar mafiya yawan bindigogin an kwato su ne daga wajen barayi da masu kokarin tayar da zaune-tsaye. Haka zalika mafarauta da sauran jama’ar gari sun ba da hadin kai wajen bin umarnin rundunar wajen mai do da bindigoginsu.

“Yanzu haka Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta kafa kwamatin bankado makaman da jama’a suka boye ba tare da izini ba. Sannan mun gano mutum 66 da suka mallaki bindigogi a jihar nan ba tare da lasisi ba, kuma ba za mu kyale duk wanda ya yi kunnen uwar shegu da umarnin da muka ba su ba, na ya kawo bindigar da ya mallaka ba. Kuma za mu yi amfani da ikon da muke da shi wajen tirsasa duk wanda ya mallaki bindiga ba bisa ka’ida ba ya kawo,” inji shi.

Rahotanni sun ce gwamnati ta dauki matakin haka ne a kokarinta na kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, wajen magance yawaitar ayyukan ta’addanci da bazuwar makamai a hannun bata-gari a fadin kasar nan.