✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda suna kama wadanda ake zargi da kisan Aled Badeh

A shekaranjiya Laraba ce ’yan sanda suka kama wadansu da ake zargi da kashe tsohon Babban Hafsan Tsaro, Iya Marshal Aled Badeh. Wata majiya ta ce…

A shekaranjiya Laraba ce ’yan sanda suka kama wadansu da ake zargi da kashe tsohon Babban Hafsan Tsaro, Iya Marshal Aled Badeh.

Wata majiya ta ce Rundunar ’Yan sanda ta Kasa za ta gabatar da wadanda ake zargin a babban ofishinta da ke Abuja a jiya Alhamis.

Samamen wanda ya samu nasarar kama wadanda ake zargin ya kunshi jami’an sojin sama da ayarin kwararru a karkashin Babban Shugaban ’Yan Sanda, Ibrahim Idris da kuma rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa.

Sanarwar da ’yan sandan suka fitar ta ce akwai ragowar wadanda ake farauta da hannu a kisan, kuma ta sha alwashin kame su nan ba da jimawa ba.

Wata majiya ta yiwu an kashe Badeh ne a wani shiri na yi garkuwa da shi da bai samu nasara ba. A baya-bayan nan ana yawan fashi da yin garkuwa tare da kashe mutane a  hanyar Keffi zuwa Bade.

An dai kashe Babban Hafsan tsaron  ne a ranar 18 ga Disamba  a hanyarsa ta dawowa daga gona, inda a cikin su uku da ke cikin motar,  Badeh ne kadai aka kashe yayin da maharan suka wuce da mutum guda shi kuma direban suka bar shi kwance cikin jini.

Daga bisani sun sako wanda suka kama bayan iyalansa sun biya kudin fansa da ake jin sun kai miliyoyin Naira.