✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji 2025: Hukumar Alhazan Yobe ta gudanar da taro don mahajjata

Tuni gwamnatin jihar ta samar da duk wasu muhimman kayayyaki don sauƙaƙa tafiyar mahajjata, waɗanda suka haɗa da: jakunkuna, kayan sawa na maza da mata…

Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe ta gudanar da wani muhimmin taro ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar Alhaji Mai Aliyu Usman kan yadda za a tsara shirye-shiryen hajiin bana daga nan gida Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki Saudiyya.

A yayin taron shugaban hukumar ya yi wa mambobin kwamitin alhazan ƙarin haske kan tsare-tsaren da aka yi don samun nasarar daidaitawa da jin daɗin alhazan da ke shirin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025.

Mai Aliyu ya ce, tuni gwamnatin jihar ta samar da duk wasu muhimman kayayyaki don sauƙaƙa tafiyar mahajjata, waɗanda suka haɗa da: jakunkuna, kayan sawa na maza da mata da kuma lambar tantancewa.

Wannan tallafi mai fa’ida yana nuna ƙudurin gwamnati na tabbatar da kwanciyar hankali, aminci, da daidaita aikin hajji na bana 2025.

Ya jaddada ƙudirin hukumar na ganin an gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali da lumana ga dukkan maniyyatan Jihar Yobe.

A yayin taron, shugaban hukumar, tare da mambobin kwamitin Hajji sun karɓi allurar rigakafin da ma’aikatan aikin hajji suka gudanar.

Wannan ya nuna yadda aka fara shirye-shiryen aikin hajji na shekarar 2025, tare da tabbatar da lafiya da amincin ga dukkan jami’ai da maniyyata.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da: Amirul Hajj, mai martaba Alhaji Abubakar Muhammad Ibn Grema (Mai Tikau), da Mohammed Mairami a matsayin sakataren kwamitin Alhaji Gana Fantami mamba a kwamitin, Sanata Alkali Jajere mamba sai mai shari’a Uwani mamba da sauran mambobin kwamitocin aikin hajji.

Taron ya kuma kasance wani dandali ga mambobin kwamitin don yin shawarwari kan muhimman dabaru da kuma fahimtar yadda za a samu gudanar da ingantaccen aikin hajji.