’Yan sanda sun kama tare da tsare wakilin kamfanin Dillancin Labarai (NAN) da ke Zariya a yayin gudanar da aikinsa.
’Yan sandan sun tsare dan Mustapha Adamu Yauri ne a lokacin da yake daukan rahoto kan wani rikicin tsakanin direban wata babbar mota da jami’an KASTELEA mai kula da hanyoyi da muhalli na Jihar Kaduna, a yammacin Talata.
Hatsaniyar ta faru ne a kan hanyar Samaru, bayan jami’an KASTELEA da ’yan sanda sun yi yunkurin dukan direban babbar motar da gora amma yaran motarsa suka ce allamabaran.
’Yan KASTELEA sun tsayar da motar direban, amma bai tsaya ba sai suka bi shi da ’yan sanda suka tsare shi neman dukan sa da gora, su kuma yaran motar suka dauko wuka don su kare ubangidansu.
— Daga daukar rahoto suka kama shi
Ganin haka sai dan jarida Mustapha Yauri ya tsaya don gudanar da binciken kan abun da ya faru ta hanyar zantawa da mutanen da suka ga abun da ya faru.
Bayan ya kammala sai ya nufi wurin da direbobin manyan motocin suka rufe hanyar da motocinsu domin ya dauki hoton yanayin da ake ciki.
A nan ne wani wanda ba ya cikin kayan sarki ya bukace shi ya ba shi wayarsa, shi kuma ya hana saboda bai san shi ba kuma bai yarda da shi ba.
— Ya gabatar da shaida amma aka ki karba
Ganin haka sai shi jami’in wanda ba ya cikin kaki ya umarci wasu ’yan sanda uku da su tafi da Mustapha ofishinsu na shiyya su tsare shi.
Dan jaridar ya gabatar da katin shaidar wuri aikinsa da na kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa( NUJ) amma dan sanda ya kawar da kai ya ce su kama shi su jefa a motarsu idan ya ki shiga.
— Sai da manya suka sa baki
Bayan sun tafi da shi sun kwace wayarsa tare da duk wani abun da yake dauke da shi, suka sa shi a bayan kanta aka tsare shi na wasu sa’o’i.
Daga baya ya nemi a ba shi wayarsa ya sanar da wurin aikinsa halin da yake ciki, su kuma suka tuntubi NUJ Reshen Jihar Kaduna inda su kuma suka tuntubi Rundunar ’Yan Sandan Jihar.
Sai da Kakakin rundunar ASP Muhammad Jalige ya kira ya nemi da a kyale dan jaridar kafin aka ba shi wayarsa da katin wurin aikisa.
Sun kuma ba shi hakuri ta bakin Babban Jami’in Yanki na Sabon Gari Abdullahi Ibrahim.