✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun tono gawarwaki 5 a Kuros Riba kan zargin maita

Wadanda suka kashe mutanen sun kuma binne su a cikin daji

’Yan sanda a Jihar Kuro Riba sun tono gawarwakin wasu mutum biyar da aka kashe bisa zarginsu da maita.

Kakakin rundunar a Jihar, Irene Ugbo, shi ne ya tabbbatar da hakan ga manema labarai a Kalaba, babban birnin jihar, ranar Juma’a.

Ya ce, “Kisan wadannan mutane tsagwaron jahilci me da gidadanci, kuma ba abu ne da za mu lamunta ba. Za mu yi dukkan bakin kokarinmu wajen ganin duk masu hannu a cikin lamarin sun fuskanci fushin hukuma.”

Aminiya ta rawaito cewa ana zargin matasan gundumar Ndong Wang da ke Karamar Hukumar Odukpani da dukan wasu mutum biyar; mata uku da maza biyu, har sai da suka mutu kan zarginsu da maita.

Mutanen da aka kashe din sun hada da Iquo Edet Eyo da Michael Robert da Etim Ekpenyong Ekpo da Akang Eyo da kuma Atim Ekpo.

Shaidun gani da ido sun ce an azabtar da mutanen kafin a kashe su, saboda ana so su amsa cewa lallai su mayu ne.

Aminiya ta kuma gano daga wajen ’yan sanda cewa wadanda suka kashe mutanen daga bisani kuma sun debi gawawakinzu zuwa cikin daji, inda suka binne su a cikin wani rami.