✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun rufe harabar Majalisar Dokokin Filato

'Yan sanda sun rufe daukacin duk wata hanyar shiga harabar majalisar dokokin jihar.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato ta rufe kofar shiga harabar Majalisar Dokokin Jihar tare da rufe daukacin ginin.

Da misalin karfe 5:00 na safiyar Laraba ne ’yan sanda masu kwantar da tarzoma suka isa harabar majalisar, inda suka yi amfani da manyan motocinsu wajen toshe babbar kofar shigarta.

Matakin na ‘yan sanda ya sa da wahala duk wanda ke tafiya a kafa ko a abin hawa ya iya samun damar shiga cikin harabar majalisar.

Sai dai har yanzu Rundunar ‘Yan Sandan ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan dalilan rufe harabar majalisar ba.

Amma Aminiya ta gano cewar matakin nasu ba zai rasa nasaba da rikicin shugabancin da ya barke tsakanin ‘yan majalisar ba.

Tuni dai majalisar ta rabu gida biyu; tsagi daya na biyayya ga Kakakin Majalisar, Yakubu Sanda sai kuma daya tsagin mai biyayya ga mai magana da yawun majalisar, Ayuba Abok wanda aka tsige a watan Oktoban 2021.

An gano cewa bangarorin biyu na iya yin arangama da juna a zauren majalisar, idan har aka ba su damar shiga tun bayan da kowannenn su ke ikirarin halaccin kujerar shugabancin majalisar.