’Yan sanda sun mayar da tsabar kudi Naira miliyan biyar da dubu dari tara da ashirin da bakwai da suka tsinta mallakar wani matafiyi a Jihar Filato.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Filato, Bartholomew Onyeka, ya mika wa iyalan wani mutum mai suna John Okeke, da ke zaune a hanyar Rukuba a Karamar Hukumar Bassa, wanda kudaden nasa suka bace bayan ’yan fashi sun tare su a hanya.
- Orubebe ya zama jagoran yakin neman zaben APC a Delta
- An kama matashi ya saci satar giyar N200,000
- Matashi zai yi wata 3 a kurkuku kan satar wayar N30,000
Kwamishinan ya mika wa iyalan kudin ne a ranar Talata, a hedikwatar rundunar da ke garin Jos.
Shi dai Mista Okeke, an yi masu fashin ne tare da wasu fasinjoji, a ranar 22 ga watan Mayun da ya gabata, a hanyar Fuskar Mata zuwa garin Jingir.
Kwamishinan ya yi bayanin cewa a lokacin da wannan al’amari ya faru, wasu daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, sun bazama cikin daji sun bar kayayyakinsu.
Ya ce ’yan sanda sun isa wajen da abin ya faru, suka ceto mutanen da abin ya rutsa da su.
Ya ce a cikin kayayyakin da ’yan sanda suka gano har da wadannan kudade Naira miliyan biyar, wadanda bayan bincike suka gano cewa mallakar Mista Okeke ne.
“A lokacin da wannan al’amari yake faruwa an kira ofishin ’yan sanda na yankin Jingir, aka sanar da su.
“Nan take Babban Jami’in ’Yan Sanda na yankin, SP Alobo E. John ya hada rundunar ’yan sanda suka isa wajen, tare da ceto mutanen abin ya rutsa da su, kuma suka fatattaki ’yan fashin.
“A cikin wadanda aka ceto din an ruga da wata mata mai suna Laraba Ibrahim, zuwa Asibitin Kwararru na Filato da ke Jos, inda aka tabbatar da rasuwarta, sakamakon harbin bindiga da ’yan fashin suka yi mata”.