✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun mamaye Majalisar Dokokin Edo

Sun rufe Majalisar bayan tsige Mataimakin Kakakin majalisar da ke goyon bayan 'yan adawa

Sa’o’i kadan bayan ‘yan Majalisar Dokoki ta jihar Edo sun tsige mataimakin kakakinsu, Hon. Yekini Idiaye, jami’an ‘yan sanda sun mamaye harabar majalisar.

‘Yan sandan sun ce sun dauki matakin ne don kauce wa yuwuwar samun tarzoma a majalisar.

An dai tsige dan majalisar ne wanda shi yake wakiltar mazabar Akoko-Edo ta daya tare da wasu takwarorinsa su hudu ne saboda nuna goyon bayansu ga dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu.

Sauran ‘yan majalisar da suka goyi bayan nasa sun hada da Hon. Emmanuel Agbaje, na majabar Akoko-Edo ta biyu da Hon. Nosayaba Okunbor na mazabar Orhiomwon ta gabas, da Hon. Dumez Ugiagbe, zababben mamba mai wakiltar mazabar Arewa maso gabashin Ovia ta daya da kuma Mr. Hon. Vincent Uwadiae, zababben dan majalisa mai wakiltar Arewa maso gabashin Ovia ta biyu.

Dukkansu dai sun nuna mubayi’arsu ne ta hanyar kai ziyara gidan Osagie din dake birnin Benin.

A wani labarin kuma, tuni ‘yan majalisar suka zabi wakilin mazabar Orhionmwon ta biyu, Hon. Roland Asoro domin ya maye gurbin Yekini a mtsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.