✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kwato mutum 15 daga ’yan bindiga a Kaduna

’Yan sanda sun kubutar da mutum 15 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna. Kwamishinan Tsaro da…

’Yan sanda sun kubutar da mutum 15 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya ce mutanen sun hada da mata uku da aka sace a kauyen Rijiya a watan Nuwamban 2020, da wasu mutum 12 da aka ceto a dajin Buruku.

“Tun lokacin masu garkuwar suke yawo da mutanen domin kada jami’an tsaro su kama su, har suka kai su Karamar Hukuamr Chikun.  Bayan samun labarin ganin mutanen ranar 1 ga Afrilu, 2021 ’yan sanda suka je suka yi ba-ta-kashi da ’yan bindigar da suka tsere suka bar mutanen,” inji shi.

Sauran mutane 12 din kuma an ceto su ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari inda jami’an tasro suka fatattaki ’yan bindigar, suka kubutar da mutanen.

A cewarsa, Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai ya yaba da kokarin ’yan sandan da suka kwato mutanen da aka yi garkuwa da su din.

%d bloggers like this: