’Yan sanda sun kubutar da mutum 15 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya ce mutanen sun hada da mata uku da aka sace a kauyen Rijiya a watan Nuwamban 2020, da wasu mutum 12 da aka ceto a dajin Buruku.
- Ya kashe abokinsa saboda musun shekarun haihuwa
- ’Yan bindiga sun kashe Shugabannin Fulani
- ‘Ni na koya wa Ali Nuhu da Adam Zango rawa’
- An fara yi wa maniyyata aikin Hajji rigakafin COVID-19
“Tun lokacin masu garkuwar suke yawo da mutanen domin kada jami’an tsaro su kama su, har suka kai su Karamar Hukuamr Chikun. Bayan samun labarin ganin mutanen ranar 1 ga Afrilu, 2021 ’yan sanda suka je suka yi ba-ta-kashi da ’yan bindigar da suka tsere suka bar mutanen,” inji shi.
Sauran mutane 12 din kuma an ceto su ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari inda jami’an tasro suka fatattaki ’yan bindigar, suka kubutar da mutanen.
A cewarsa, Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai ya yaba da kokarin ’yan sandan da suka kwato mutanen da aka yi garkuwa da su din.