✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kwato bindigogi daga hannun kasurgumin dan fashi a Imo 

Wanda ake zargin ya bayyana yadda suka addabi mutane a yankin.

An kama wani kasurgumin dan fashi da makami biyo bayan wani samame da jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Imo suka kai maboyarsu. 

Kakakin rundunar a Jihar, CSP Mike Abattam, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a Owerri ranar Talata.

A cewarsa, “A ranar 26/10/2022 da misalin karfe 09:00, jami’in dan sanda mai kula da ofishinmu na Oguta ya samu rahoton yin sata, nan take tawagarsa ta kai dauki domin gano tare da kamo wadanda suka aikata wannan laifin.

Sanarwar ta kara da cewa, “Bayan tattara bayanan sirri masu inganci, a ranar 27/10/2022 da misalin karfe 12:00 na rana, an kama wani Nnura Henry Afam mai shekaru 34 dan asalin kauyen Umayyad da ke Karamar Hukumar Oguta ta Jihar Imo.

“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ubangidansa ne, mai suna Ebuka ya umarce shi da ya shiga gidan da daddare ya sace kadarorin gidan tare da kai kayan zuwa gidansa (Ebuka).

“Ya kuma ce suna cikin gungun ‘yan fashi da makamin da ake yi wa lakabi da “Small Witch” kuma shi ne shugaban kungiyar da suka addabi al’umma a Karamar Hukumar Oguta da kewaye.

“Wanda ake zargin da ya hango ‘yan sanda daga nesa suna tunkarar gida, nan take ya kulle kofar daga ciki, ya tsere ta kofar baya zuwa cikin daji, amma sai da aka bude kofar, aka bincika aka gano wadannan abubuwan.

“Abubuwan da aka samu sun hada da bindiga kirar hannu guda uku, harsashi guda 46, bindiga AK-47 guda 72 da kuma harsashi mai tsayin 5.56mm.”

Ya ce jami’an rundunar sun baza koma don kamo ragowar wadanda suka tsere don gurfanar da su a gaban kuliya.