✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kubutar da fasinjoji 8 da aka sace a Kuros Riba 

Kakakin ’yan sandan ta musanta zargin cewar makiyaya ne suka sace fasinjojin.

’Yan sanda a Kuros Riba sun samu nasarar kubutar da wasu matafiya takwas daga cikin tara da aka yi garkuwa da su a hanyar Ogoja zuwa Ikom a ranar Talata.

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Irene Ugbo, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Laraba a Kalaba.

SP Irene ta ce tun kafin kubutar da su, daya daga cikinsu ya samu nasarar tserewa daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Kakakin ‘yan sandan ta kuma yi watsi da rade-radin cewa makiyaya ne suka kai harin.

A cewarta, “Takwas daga cikin wadanda harin ya rutsa da su yanzu haka suna hannun jami’an tsaro yayin da mutum cikon na tara ya tsere.

“Rahotanni na cewa makiyaya ne suka yi garkuwa da su, ba gaskiya ba ne; lamarin fashi da makami ne kawai,” in ji ta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Sule Balarabe, wanda ya tabbatar da sace fasinjojin a ranar Talata, bai bayar da takamaiman adadin wadanda abin ya shafa ba.

Sai dai Kwamishinan ya tura wata tawaga ta musamman, ciki har da jami’an ’yan sanda masu yaki da masu garkuwa da mutane zuwa yankin.

Wani da abun ya faru a kan idonsa, ya kuma shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane tara a kan babbar hanyar da ke tsakanin kauyen Okomita da Uyangha, a kusa da Kalaba.

Ya ce ‘yan bindigar wadanda suka fito daga ciki daji sun rika harbin motoci don tilasta musu tsayawa.

Haka kuma, ya ce wasu daga cikin fasinjojin motocin sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga.