✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe ‘yan ta’adda 2, sun kwato makamai a Katsina

An dakike harin ne yayin da maharan ke shirin yi wa kauyen tsinke.

’Yan sanda sun kashe wasu ’yan ta’adda biyu tare da kwato makaman ’yan ta’addan suka nemi kai hari a garin Yasore da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya shaida wa manema labarai a Katsina cewa ’yan ta’addan sun yi ta harbi da bindiga kirar AK-47 a kauyen Yasore da misalin karfe 07:30 na ranar Alhamis.

Ya ce DPO na Batsari ya jagoranci ayarin ’yan sanda da na ’yan banga zuwa yankin inda suka yi musayar wuta tare da samun nasarar dakile su.

Kakakin rundunar ya ce sun gano gawarwakin ’yan ta’adda guda biyu da bindigogi da alburusai da da wayoyin hannu guda biyu da laya, da tsabar kudi Naira 2,580 a hannun miyagun.

“Da yawa daga cikin ’yan ta’addan sun tsere da raunin bindiga,” in ji shi.

Kakakin ya yi kira ga al’ummar yankin da su kai rahoto ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da duk wanda aka samu ko aka gani da raunin harbin bindiga.