Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta ce ta yi nasarar kashe wasu ’yan fashi biyu yayin musayar wuta a yankin Okokomaiko da ke jihar.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi.
- EFCC ta yi gwanjon kadarorin su Diezani a kasuwa
- A karon farko, an ba Bahaushe Kwamishina a Kuros Riba
“Suna hangen ’yan sandan suka bude wuta, a sanadin haka ne biyu daga cikinsu suka rasa rayukansu, yayin da sauran suka tsere da raunuka.
“An dauki hotunan wurin da lamarin ya faru, an dauke gawarwarkin don gudanar da bincike a kansu,” in ji shi.
Hundeyin, ya ce caji ofis din ’yan sanda na yankin Okokomaiko sun samu kiran agaji da misalin karfe 2:30 na daren ranar Asabar, cewar wasu ’yan fashi sun shiga wani sashe na na’urar kamfanin Airtel da nufin yin sata.
Ya ce ba jimawa da samun kiran aka aike da jami’an rundunar zuwa yankin.
Kakakin ya kara da cewar rundunar ta baza jami’anta don cafke ragowar da suka tsere.