✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 4 a hanyar Jos

An cafke wata mace da ta kware wajen safarar makamai a Kaduna.

Rundunar ’yan sanda ta Operation Yaki ta hallaka ’yan bindiga hudu a kan hanyar Saminaka zuwa Jos a Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne bayan ’yan sandan sun hangi wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a cikin wata mota kirar Sharon a kan hanyar zuwa Jos.

Sanarwar da kakakin ’yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya fitar ta ce dubun ’yan bindigar ta cika ne lokacin da suke kan hanyarsu ta safarar wasu makamai.

Ya kara da cewa rundunar ’yan sandan ta yi dauki-ba-dadi da ’yan bindigar na tsawon minti 30 a cikin daji.

Bayan dauki-ba-dadi ne suka yi nasarar kashe hudu daga cikin ’yan bindigar, suka kwato bindiga kirar AK-47 guda uku da sauran makamai da kuma harsasai.

Har wa yau, ya ce samamen ya kai ga cafke wata mace guda daya da ta kware wajen safarar makamai ga bata-gari a Kaduna.

A cewarsa, tuni suka fara gudanar da bincike kan lamarin, don samun bayanai daga matar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Yekini A. Ayoku, ya jinjina wa ’yan sandan kan nasarar da suka samu a kan ’yan bindigar.