✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 38 a Katsina

Sai dai ’yan sanda biyar sun rasa rayukansu.

Akalla ’yan bindiga 38 rundunar ’yan sanda ta kashe a Jihar Katsina yayin da ta kame wasu miyagun mutanen 999, wadanda ake zargin suna da hannu wajen aikata muggan laifuka akalla 600.

Kwamishinan ’yan sandan jihar ta Katsina Sunusi Buba ne ya bayyana samun nasarorin, yayin karin bayani kan ayyukan da suka gudanar a cikin shekarar 2021 da aka yi bankwana da ita.

Sai dai Sunusi Buha ya ce a yayin namijin kokarin murkushe gungun masu aikata laifukan ’yan sanda biyar sun rasa rayukansu.

Dangane da daruruwan masu aikata laifukan da suka cafke kuwa, kwamishin ’yan sandan ta hannun mai magana da yawunsa SP. Gambo Isah, ya ce 874 daga cikin 999 da suka cafke din suna fuskantar shari’a a kotuna.

Ya kara da cewa, an kame mutum 157 da ake zargi da ta’adar fashi da makami yayin da tuni an gurfanar da 145 daga cikinsu, inda kuma ake ci gaba da gudanar da bincike a kan 12.

“An kuma kama mutum 65 da ake zargi da ta’addancin garkuwa da mutane kuma an gurfanar da 63 daga cikinsu, inda ragowar biyu ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.”

“An kama mutane 244 da ake zargi barayin shanu ne, kuma daga cikinsu 230 sun gurfana a gaban kotu yayin da muke ci gaba da bincike a kan 14.

“Mun kuma kwato dabbobin kiwo daga hannun wadanda ake zargin, ciki har da shanu 867, tumakai 352, awakai 24 da kuma jaki daya.

Kwamishinan ya kara da cewa, “akwai kuma mutum 246 da aka kama kan zargin aikata laifukan da suka danganci fyade da sauran laifuka masu nasaba da cin zarafi, yayin kuma mun samu nasarar ceto mutum 63 da aka yi yunkurin safararsu.

Bayanai sun ce an ceto mutane 215 da aka sace daga hannun ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a shekarar 2021 da aka yi bankwana da ita.

Katsina na daga cikin Jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya da suke fama da matsalar hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya tilastawa dubban mutane tserewa daga muhallansu, inda was uke gudun hijira a sassan jihar ta Katsina, a yayin da wasu kuma suka tsere zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

A baya bayan nan ne kuma, gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya sake yin kira ga al’ummar jihar tasa, da su tashi tsaye domin bai wa kansu kariya da kuma tunkarar barazanar ’yan bindiga da ke ci gaba da kisan jama’a, cin zarafi da kuma yin garkuwa da mutane babu kakkautawa.