✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga 2 a Bauchi

'Yan sandan sun ceto matashin da maharan suka yi kokarin sacewa.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta yi nasarar kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Rafin Gora da ke Karamar Hukumar Ningi inda ta kuma kubutar da wani matashi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a ranar Lahad.

SP Wakil ya bayyana cewa ’yan bindigar dauke da bindigogi sun kai farmaki gidan wani mazaunin unguwar Rafin Gora, inda suka yi yunkurin yin garkuwa da dansa mai shekara 28.

“Wanda abun ya rutsa da shi ya tsallake rijiya da baya da aka yi yunkurin sace shi, sai dai sun harbe shi a ciki yayin da yake kokarin tserewa.

“Jami’an ‘yan sanda tare da gungun ‘yan banga sun yi gangamin zuwa wurin domin tunkarar su da harbin bindiga,” in ji shi.

Ya kara da cewa jami’an sun mayar da martani ta hanyar artabu, lamarin da ya sa maharan suka tsere da raunuka.

“Biyu daga cikinsu sun mutu, yayin da aka kwato AK47 guda daya daga hannunsu.

“An ceto wanda lamarin ya rutsa da shi mai shekara 28, kuma nan take aka kai shi Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kudu domin yi masa magani.

Ya kara da cewa, an fara farautar wadanda ake zargi da guduwa domin su fuskanci doka.