✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe mutum 1, sun kama masu laifi 6 a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar dakile ayyukan masu garkuwa da mutane tare da kashe mutum ɗaya daga cikinsu. 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar dakile ayyukan masu garkuwa da mutane tare da kashe mutum ɗaya daga cikinsu.

Haka kuma, sun kama wasu mutane shida da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

A cewarsa, sun kama mutum uku da ake zargi da aikata fashi da makami, tare da wasu uku da ake zargi da safarar bindigogi.

An kuma samu kayayyaki kamar bindigogi guda biyu, bindiga ƙirar gida guda ɗaya da kuma harsasai 216.

ASP Mansur, ya ce a ranar 8 ga watan Disamba, jami’an ’yan sanda daga ofishin yanki Kasuwar Mata a Sabon Gari sun kai farmaki wani gidan karuwai da ke Titin Nupe bayan samun rahoton sirri.

A waje , sun kama wani Adamu Yahaya mai shekara 35 tare da bindiga ƙirar gida, kwanson harsasai, da sarƙa.

Har ila yau, a ranar 8 ga watan Disamba, jami’an ‘yan sanda na Barnawa sun kama wasu mutum biyu; Andrew Emmanuel da Mendwas Peter Bulus.

An same su da bindiga ƙarama, wayoyi biyu ƙirar Infinix, da kuma tabar wiwi.

Yayin bincike an gano ’yan fashi da makami ne.

A ranar 9 ga watan Disamba, jami’an da ke Dan Magaji Zariya sun kama wasu mutum uku a babbar hanyar Kano zuwa Kaduna yayin wani sintiri.

An same su da harsasai 216 da kuma kwanson harsasai.

Mutanen sun haɗa da Buhari Suleiman daga Labar, Jamil Yakubu daga Katsina, da Aliyu Abdullahi daga Tashan Jaji.

Bayan bincike, Jamil Yakubu ya bayyana cewa ya sayi harsasai guda 50 a Katsina.

Ya kuma ce Buhari Suleiman ne ke siyar masa da harsasan.

A ranar 10 ga watan Disamba, jami’an yankin Dama Kasuwa sun kashe wani ɗan bindiga a waga musayar wuta a Tudun Geshere.

Sauran ’yan bindigar sun tseree cikin daji tare da raunukan harbin bindiga.

Wannan nasarar ta samu ne da haɗin gwiwar ’yan sa-kai na CJTF da KADVIS.

Kwamishinan ’yan sandan, Abdullahi Ibrahim, ya yaba wa jami’an bisa ƙwarewarsu, tare da jinjina wa al’umma kan bayar da bayanai masu muhimmanci da suka taimaka wajen samun nasarar.