Rundunar ’yan sanda a Jihar Filato ta kashe wasu mutum biyu da ake zargi da ta’adar garkuwa da mutane a garin Gindiri na Karamar Hukumar Mangu ta jihar.
ASP Ubah Ogaba, jami’in hulda da al’umma na rundunar, shi ne ya inganta rahoton cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a birnin Jos.
- Jan Kati: An dakatar Messi tsawon wasanni 2
- Mahara sun yi awon gaba da Hakimi a Adamawa
- Zamfarawa sun yi artabu da ’yan bindiga har maboyarsu
A cewarsa, an kashe miyagun ne a yayin wani karanbatta da suka yi da jami’an ’yan sanda da tsakar rana.
Ya ce da dama daga cikin gungun masu ta’adar ta garkuwa sun tsere da raunuka na harsashin bindiga.
A kokarin da muke yi na dakile aukuwar miyagun laifuka a Jihar, mun kaddamar da farauta a kan wasu gungun masu satar mutane da suka yi garkuwa da wasu mutum biyu a yankin Chanso da ke gundumar Gindiri a Karamar Hukumar Mangu.”
“Rukunin jami’anmu masu liken asiri da tattaro bayanan sirri ne a yau da misalin karfe 1 na rana suka afka maboyar masu garkuwa inda suka kaure da fada da hakan yayin sanadiyar kashe biyu daga cikinsu.”
Sauran mambobin kungiyar ta masu garkuwa da mutane sun tsere da raunuka daban-daban na harsashin bindiga,” in ji shi.
Ogaba ya ce an kubutar da mutanen biyu da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba kuma an sada su da ’yan uwansu.
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Ogaba ya bayar da tabbacin cewa za su zage dantsensu domin gano sauran ’yan kungiyar da suka tsere.
Ya yi kira ga al’umma da su rika shigar da muhimman bayanai ga jami’ansu da za su taimaka wajen bankado masu nufin aikata sharri a tsakaninsu.