Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa tare da hadin gwiwar wasu mafarauta ta kashe wani mai garkuwa da mutane tare da ceto mutum biyun da aka sace a Karamar Hukumar Toungo da ke Jihar ranar Lahadi.
Kakakin rundunar a Jihar, Suleiman Nguroje ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Litinin.
- Boko Haram ta kashe mutum 10 a yankin da ISWAP ta mamaye a Borno
- Birtaniya ta dakatar da daukan ma’aikatan lafiya daga Najeriya
Ya ce hakan na cikin irin nasarorin da suke samu a kokarinsu na yaki da satar mutane da fashi da makami da satar shanu da kuma rike makamai ba bisa ka’ida ba.
Ya ce, “Mun kashe wani mai garkuwa da mutane lokacin da ya isa wajen da zai karbi kudin fansa Naira miliyan biyu daga iyalan wadanda ya sace.
“Lokacin da masu garkuwar suka hangi jami’anmu, sai suka bude musu wuta saboda kada a kama su.
“Nan take aka ci gaba da musayar wuta, inda a cikin haka, aka kashe daya daga cikinsu, ragowar kuna suka gudu da harbi a jikinsu,” in ji shi.
Suleiman ya kuma ce jami’an nasu sun sami nasarar kubutar da mutum biyun da aka sace daga hannun masu garkuwar, wadanda dukkansu mazauna kauyen Mayo Sasum ne da ke Karamar Hukumar ta Tounga.
Ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Afolabi Babatola ya jinjina wa jami’an nasu a yankin bisa samun wannan nasarar tare da hadin gwiwar mafarautan. (NAN)