✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe mahauta bisa zargin satar shanu a Auyo

Jami’an ’yan sanda a yankin karamar Hukumar Auyo da ke Jihar Jigawa sun harbe wasu mahauta biyu har lahira yayin da daya ya samu raunin…

Jami’an ’yan sanda a yankin karamar Hukumar Auyo da ke Jihar Jigawa sun harbe wasu mahauta biyu har lahira yayin da daya ya samu raunin harsashi a jikinsa, yana kwance a asibiti rai a hannun Allah.
Mahautan, wadanda aka ce fataken shanu ne, sun sayo shanu daga wani kauye da daddare suna kan hanyarsu ta komawa gida ne, ’yan sandan suka yi masu kwantan bauna suka bude masu wuta.
Kamar yadda bincike ya nuna, mahautan an ba ’yan sanda labarin cewa sun sayo shanun sata ne; lamarin da ya sa aka samu cece-kuce tsakanin ’yan sandan, a lokacin da suke kokarin tuhumar su, lamarin da ya sa daya daga cikin jami’an ya bude masu wuta, ya halaka biyu daga cikinsu.
Kakakin rundunar ’yan sandan na Jihar Jigawa, DSP Abdu Jinjiri ya tabbatar da faruwar al’amarin. Ya ce tuni ma hukumarsu ta cafke jami’in day a yi harbin kuma suna nan suna bincike a kan lamarin, domin gano gaskiyar lamarin kafin a dauki matakin da ya dace. Ya kuma musanta labarin cewa mutane biyu aka halaka, ya ce mutum daya ne ya rasa ransa daga cikin mahautan uku, yayin da mutane biyu suke kwance a asibiti, suke shan magani. Ya kuma kara da cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata da misalin karfe bakwai na yamma.
Kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilinmu, mahautan uku sun hada da Isah Abdulhamidu da Malam Abdullahi da kuma Musa Mahauci. Majiyar ta ce shi Isah Abdulhamid ne ya rasa ransa nan take, yayin da Abdullahi ya rasu bayan kwana daya da faruwar lamarin a asibiti.
Wani matashi mazaunin garin na Auyo ya ce ba domin taimakon manyan gari ba da tuni ofishin na ’yan sanda ya koma toka saboda dandazon da matasa suka yi, dauke da makamai da sanduna da galan-galan na man fetur, suna kokarin cinna masa wuta suna jifar jami’an da duwatsu.
Amma duk da haka kakin na ’yan sanda ya karyata labarin cewa matasan sun nemi tarwatsa ’yan sandan daga ofishinsu. Ya ce babu wani labari makamancin haka kuma babu wani da aka kama a kan waccan rigima.