Rundunar ‘yan sanda a jihar Kebbi ta kashe wani ɗan bindiga tare da cafke wasu mutane biyu a yayin da suka kai farmaki a unguwar Danko Wasagu da ke jihar.
Bayanai sun ce tawagar ‘yan bindigar da ke kan babura sun kai farmaki a garin Kurgeye da ke cikin Unguwar Danko a ƙaramar hukumar Wasagu a jihar Kebbi.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar, ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wani Malam Danladi tare da ɗansa Bello Danladi a cikin unguwar.
“Lokacin da muka samu rahoton, ayarin ‘yan sandan tafi da gidanka 36 da ke aiki na musamman tare da haɗin gwiwar ’yan banga, sun yi gaggawar mayar da martani tare da fatattakarsu.
“An yi musayar wuta a tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigar,” in ji shi.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an samu nasarar ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya ɗauke da alburusai da babur ƙirar Bajaj daga hannun ‘yan bindigar da suka tsere.
A wani rahoton kuma, rundunar ‘yan sandan ta ce, tawagar ‘yan sanda da ke sintiri na haɗin gwiwa da ‘yan banga a kan hanyar Ribah zuwa Kanya, sun kama wani Isiya Alhaji Usman da Yunusa Yusuf daga ƙauyen Auda da ke yankin Danko/Wasagu a jihar.
Ya ƙara da cewa ‘yan sandan sun ƙwato bindigar K2 guda ɗaya da bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya tare da tarin alburusai uku da harsasai 66 daga hannun mutanen biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka addabi yankin.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kebbi, Bello M. Sani ya yaba wa yadda rundunar ta nuna ƙwazo, sannan ya buƙaci su ƙara himma wajen tabbatar da tsaro a jihar da kewaye.