✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun karyata jita-jitar shigowar makamai a Ibadan

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo, Leye Oyebade, ya tabbatar wa mazauna birnin Ibadan da kewaye cewa, rundunarsa ta aika da jami’anta domin binciken gano…

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo, Leye Oyebade, ya tabbatar wa mazauna birnin Ibadan da kewaye cewa, rundunarsa ta aika da jami’anta domin binciken gano gaskiyar labarin da ake bazawa cewa, wasu manyan motoci dauke da makamai sun shigo cikin wasu unguwanni a cikin birnin na Ibadan. Mazauna birnin na Ibadan sun fara firgita ne a lokacin da suka saurari wani shiri na gidan rediyon Fresh FM da karfe 12 na ranar Juma’a da ta wuce, a inda wani mutumi dan Najeriya ya bugo waya daga kasar Jamus yake cewa, a daidai wannan lokaci akwai wasu manyan motoci dauke da makamai da aka girke guda daya a unguwar Sabo mazaunin Hausawa ta biyun kuma a garejin Iwo Road duka a cikin birnin Ibadan.
Wannan ne ya sa rundunar ‘yan sanda ta hanzarta daukar matakan aikewa da jami’anta na sashen yaki da ta’addanci da yaki da masu satar mutane da fashi da makami da sashen binciken bama-bamai da sauran jami’ai da aka baza su cikin wadannan unguwanni biyu da sauran unguwanni, domin yin binciken gano gaskiyar wannan jita-jita da ta bazu a gari inji Kwamishinan ‘yan sandan wanda ya ce babu wata babbar mota ko karama da suka gano a binciken na su, amma suna nan suna ci gaba da yin bincike.
CP Leye Oyebade, ya nemi jama’a su kwantar da hankali a kan wannan jita-jita, wacce ya tabbatar da cewa, bincikensu ya kai ga ziyartar ofishin gidan rediyon na Fresh FM da ya fara yayata labarin.
Ya ce rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da daukar matakin kare lafiya da dukiyoyin jama’a, domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
 Wakilinmu ya garzaya zuwa fadar Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru, domin jin ta bakinsa dangane da wannan al’amari da aka danganta shi da aukuwa a cikin masarautarsa.
A cewar Sarkin Hausawan: “Jim kadan da jin wannan labari ne hadaddiyar kungiyar gyara da ci gaban gari a karkashin jagorancin Alhaji danjuma Garba Garas ta baza membobinta zuwa ciki da wajen unguwar Sabo da suka fara aikin bincike tun kafin jami’an ‘yan sanda su isa wurin, amma babu abin da aka gano a dangane da hakan. Duk da yake mun yi farin ciki da zuwan jami’an tsaron, sai dai ba mu ji dadin yadda aka turo su ba tare da saninmu ba. Kamata ya yi a fara sanar da mu kafin isowarsu, domin mu ba su cikakken hadin kai a kan binciken da suke yi. Ina kyautata zaton wasu ne suka yi dabarar ambaton sunan unguwar Sabo da suka danganta ta da wannan al’amari, domin su bata mana suna da shafa mana bakin fenti a kan al’amarin tsaro.”
Wakilinmu ya ce, har zuwa lokacin rubuta wannan labari babu wani karin bayani da ya fito daga ofishin ‘yan sanda da ya shafi wannan al’amari.