✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama ‘yan ci-ranin Nijar da Mali 12 a Kano

'Yan ci-ranin an kamo su ne daga kasar Saudiyya

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kama wasu bakin haure 12 ‘yan asalin kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar.

Haka kuma ta tabbatar da kama wasu mutum  33 da ake zargi da aikata laifuka.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mohammed Usaini Gumel, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce bakin hauren sun kunshi ‘yan kasar Mali bakwai da ‘yan Nijar biyar da aka koro daga Saudiyya.

A cewarsa, an gano su ne a wani gida da ke unguwar Hotoro ‘Yandodo a Kano.

“Bakin hauren sun samu raunuka ta hanyar yankan reza don gujewa kamu daga hukumomin Saudiyya.

“An kama sauran mutum 33 da ake zargi da laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, sata, garkuwa da mutane da kuma mallakar haramtattun makamai da sauransu,” in ji Kwamishinan.

Kayayyakin da aka kwato, ya ce sun hada da wayoyin hannu guda 46, layin waya 21, wukake, katako, bindigar wasan yara guda daya da kuma tarin manyan makulli.

Sauran sun hada da kwaya guda 79, kullin ganyen tabar wiwi guda 98 da sauransu.

Ya ce za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.