✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da lalata yara 91

An tuhumi mutumin da lataya kananan yara 91 a cibiyoyin kula da yara a kasar.

’Yan sanda a kasar Australia sun tuhumi wani tsohon ma’aikacin kula da yara da ake zargi da laifin yin lalata da yara 91.

’Yan sanda sun bayyana laifin a matsayin abu mafi girma a ranar Talata.

Sun kuma ce laifukan sun faru ne a cibiyoyin kula da yara 10 daban-daban tsakanin 2007 zuwa 2022.

Jami’an sun kara da cewa ana tuhumarsa da laifuka guda 1,623, da suka hada da 136 na fyade da kuma laifuka 110 na jima’i da wani yaro dan kasa da shekaru 10.

Jami’an ’yan sanda sun bankado wasu hotuna a wayar mutumin mai shekara 45, kuma sun ce suna da kwarin gwiwar samun wasu bayanai.

’Yan sandan sun kuma ce mutumin ya tsallake duk tsauraran matakan bincike da ake bukata don yin aiki tare da yara a Australia.

Wani babban jami’in ’yan sanda mai binciken ya ce, “Ya wuce tunanin kowa abin da mutumin ya aikata.

“Zan iya cewa, bayan tsawon lokaci wannan lamari abun tsoro ne, amma muna bincike don gurfanar da shi a kotu.”