✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama mutum uku masu garkuwa da mutane a Jigawa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta gabatar da wadansu mutum hudu da ake zargin masu yin garkuwa da mutane ne da aka kama su a…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta gabatar da wadansu mutum hudu da ake zargin masu yin garkuwa da mutane ne da aka kama su a lokacin da suka yi fashi a gidan wani Bafillatani bayan sun bukaci ya ajiye musu Naira miliyan daya, amma da hakan ba ta samu ba suka suka kwace masa Naira dubu 250.
Matasan sun hada da Abubakar Sani, wanda ake yi wa lakabi da bingel da Sani Alhaji Amadu da kuma shugabansu Sani Isyaku wanda ake yi wa lakabi da Martaba, kuma an kama su ne a karamar Hukumar Gwaram da ke jihar kuma dukkansu Fulani ne.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar SP Audu Jinjiri wanda ya gabatar da wadanda ake zargin tare da sauran wadanda ake zargi da aikata laifuffuka ya fadi a wata sanarwa a shekaranjiya Laraba cewa rundunar tana neman wadansu mutum biyu da suka tsere da ake zargin suna da hannu a cikin garkuwa da mutanen.
Sauran wadanda aka gabatar sun hada da wadansu matasa da ake zargin sun dade suna lalata da kananan yara da kuma wadansu da ake zargin ’yan luwadi ne.
SP Audu Jinjiri ya bayyana cewa an kama wani mai suna Malam Isah Sani Hadeja mai kimanin shekara 45 kan zargin yin lalata da wata yarinya ’yar shekara 10 a garin Hadeja, kuma wanda ake zargin ya furta cewa ya jima yana aikata irin wannan ta’asa a Hadeja sai a wannan karo ne asirinsa ya tonu. Sai dai ya nemi ’yan sandan su sassauta masa ba zai sake ba, saboda yana da ’ya’ya takwas da mata da yake kula das u.
Sannan an kama wadansu matasa su hudu daga yankin Gumel bisa zargin aikata luwadi da junansu da suka hada da Zaharaddin Magaji da Auwalu Aliyu da Auwalu Jibrin da Zakari Idris da Najib Salisu, sai dai sun ce sun riga sun daina wannan danyen aiki tun shekara takwas da suka wuce.
Amma kakakin ’yan sandan ya ce dukansu tuban muzuru suka yi, inda suka dawo ruwa kuma za a gabatar da su a gaban alkali domin yanke musu hukunci.
Sai kuma wani matashi a yankin Birnin Kudu mai suna Shukurana da ake zargi da yin fyade da wata Bafillatana mai kimanin shekara 45 a kan hanyarta ta zuwa rugarsu bayan ta dawo daga Birnin
Kudu. Matashin mai kimanin shekara 25 ya ce tsautsayi ne ya sa ya aikata hakan kuma ya nemi ’yan sanda su rufa masa asiri wannan ne karan farko da ya aikata hakan.