✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama mutum 3 da jabun kuɗi N129bn a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum uku da aka samu da jabun kuɗi har Naira biliyan 129.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum uku da aka samu da jabun kuɗi har Naira biliyan 129.

Kakakin rundunar, SP Haruna Kiyawa ne, ya bayyana wa manema labarai a Kano ranar Talata cewa jabun kuɗin sun haɗa da Dalar Amurka, CFA da Naira.

Ya ce adadin kuɗin da aka ƙwato sun haɗa da dala 3,366,000, CFA51,970,000, da Naira 1,443,000.

SP Kiyawa, ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin, suna hannun ‘yan sanda kuma suna taimakawa wajen bincike don gano inda ake buga jabun kuɗin.

Baya ga kuɗin, ’yan sanda sun kuma k6wato harsasai guda shida, Adaidaita Sahu guda uku, babura guda takwas da kuma jakunkuna uku ɗauke da tabar wiwi.

Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da ƙwayoyi 250 na diazepam, tumaki 278, da shanu guda bakwai.

Kiyawa, ya ce kama waɗannan mutane na nuna yadda rundunar ke ƙoƙarin yaƙi da laifuka a Kano.

Ya ƙara da cewa rundunar ta magance manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, da kuma rikicin daba.