Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta yi katarin kama matoci biyu dauke da makamai a sassan jihar daban-daban.
Mai Magana da Yawun Rundunar, Mista Muhammad Shehu shi ne ya bayar da tabbacin kamun a garin Gusau.
Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa kayan da suka kama sun hada da bindiga kirar AK47 guda uku da karamar bindigar fistol da bindigar gargajiya da kuma harsasai masu yawa.
Ya bayyana cewa sauran makaman sun hada da kudi Naira dubu dari da uku da 435 da katin ATM da katunan zabe da kayan sojoji na bogi da kan sarki na kungiyar dillalan shanu ta Najeriya da ke karamar hukumar Buruku a jihar Filato.