Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wadansu matasa uku da take zargi da hannu a kisan wani matashi mai hidimar kasa a gidan dan takarar Gwamnan Jihar na PDP, Honarabul Dabid Ombugadu da ke Akwanga a makon jiya.
Kakakin Rundunar, ASP Ismail Usman ne ya sanar da haka lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu dangane da batun a ofishinsa da ke hedikwatar rundunar a Lafiya.
A cewarsa jim kadan da aukuwar lamarin sai jami’ansu suka fara gudanar da bincike, inda daga baya suka kama wadanda ake zargi da kashe mai hidimar kasar mai suna Samuel Makene, inda suka yi amfani da wukake suka farke masa ciki a gidan dan takarar Gwamnan na PDP Dabid Ombugadu a lokacin da yake kokarin hana su kwashe wasu kayayyaki masu amfani daga gidan dan siyasar a yayin ganganmin yakin neman zabensa a Shiyyar Akwanga.
Ya ce “A yanzu da nake magana da kai mun kamo matasa uku da ake zargi da aikata danyen aikin kuma tuni muka turo su fannin bincikar manyan laifuffuka na rundunarmu a nan Lafiya don ci gaba da gudanar da cikakken bincike a kansu. Kuma da zarar mun kammala binciken za mu gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu don fuskantar hukunci daidai da laifin da suka aikata,” inji shi.
Kakakin Rundunar ya yi amfani da wannan dama inda ya tabbatar wa iyalan mamacin cewa rundunar za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa wadanda ake zargi da kisan dan uwansu da sauran masu aikata laifuffuka a jihar sun fuskanci hukuncin da ya dace da laifinsu, domin hakan ya kasance darasi ga ire-irensu da ke aikata ko niyyar aikata irin wadannan miyagun laifuffuka.
Idan za a iya tunawa a karshen makon jiya ne wadansu matasa da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka hallaka mai hidimar kasar Samuel Makene.