✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kama masu luwadi 5 a Kano

Sun bayyana yadda suka yi ta yaudarar yaron suna lalata da shi.

’Yan sanda a Jihar Kano sun kama wasu mutane biyar da suka yi lalata da wani matashi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama mutanen ne bayan iyayen yaron sun kai mata korafi kan yadda mutanen suka rika yaudarar shi zuwa wurare daban-daban suna yin lalata da shi ta bubura.

Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bayan matashin mai shekara 20 ya yi ta fama da matsanancin ciwon ciki ne innarsa ta nemi jin ainihin abin da ke damunsa.

“Da ta bincika sai ya bayyana mata cewa mutanen ne suka yaudare shi suka yi ta lalata da shi ta dubura a lokuta da dama, sakamakon haka ne ya kamu da ciwon cikin.”

Kayiwa ya ce an kai matashin Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, da ke Kano inda aka yi masa jinya aka kuma sallame shi.

A cewarsa bayan Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya da ba da umarni, an kamo wadanda ake zargin sun kuma amsa cewa sun aikata laifin.

Ya bayyana cewa daya daga cikin mutanane mai shekara 33 ya bayyana wa ’yan sanda cewa shi ne ya fara yaudarar yaron ya yi lalata da shi.

Jami’in dan dansana ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da wadanda ake zargin  a gaban kotu.