Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama matasa 49 da take zargi da laifin kwashe dukiyar mutane a rukunin shaguna na Gidan Jaridar Triumph da sunan ganima.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar tare kuma ya raba wa manema labarai a Kano.
- Farashin gas din girki da man jirgin sama ya karye
- Kasashen da suka rage a Gasar Kofin Duniya ta ’yan kasa da shekaru 20
Tun bayan zuwan sabuwar gwamnatin Jihar Kano ta kafa kwamitin kar ta kwana da zai binciki yadda wasu tsirarun mutane suka mallaki wasu kadarorin gwamnati ba bisa kaida ba wanda tuni kwamitin ya fara gudanar da rushe rushe a irin wadannan wurare.
Kiyawa ya bayyana cewa rundunarsu ta samu rahoton wasu mutane sun far wa sabbin shagunan gidan jaridar inda suka kwashe kayayyaki na dubban Nairori.
A cewarsa, hakan ya sa Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel ya aike da taawagar wanzar da zaman lafiya wurin inda kuma wadanda ake zargi suka tsere yayin da aka kama wasu daga cikinsu.
Kiyawa ya kara da cewa, an yi nasarar samun wasu kayayyakin da matasan suka kwashe da sunan ganima da suka hada da kofofi da tagogi da na’urar sanyaya daki kirar Kamfanin LG da sauransu.
A cewar Kiyawa, tuni aka fara kaddamar da bincike a kan lamarin inda kuma Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano yake shawartar iyaye da sauran shugabanni al’umma da su gargadin yaransu dangane da kwashe dukiyar mutane domin yin hakan sata ce kai tsaye wanda kuma shari’a ta tanadi hukunci a kansa.