✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama masu kwacen waya 18 a Kano

Rundunar ta ce za ta ci gaba da aiki don maganin bata gari a jihar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama masu kwacen waya 18 wadanda suka shirya kaddamar da hare-hare kan al’ummar jihar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Usaini Gumel ne, ya bayyana haka a ranar Litinin.

Gumel, ya ce “Wadanda ake zargin gungun ‘yan wata kungiya ne da suka yi shirin kai wa jama’a hari .”

Kwamishinan, ya ce an kama barayin ne a wani samame daban-daban a a maboyarsu da ke jihar.

Ya ce an kama su ne a yankunan Mazaunar Tanko, Dandishe, Kofar Dan Agundi, Kofar Mata da kuma Filin Idi.

Sauran wuraren da aka gano a matsayin maboyarsu sun hada da Kofar Na’Isa, Kwanar Diso, Kukar Bulukiya da Dorayi Babba.

Ya ce, abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin yayin bincike sun hada da muggan makamai, kwayoyi da kuma tabar wiwi.

Gumel, ya ce za su gudanar da bincike a kan su domin samun bayanai da za su takmaka ga kama wasu da ke da hannu a fashin waya a jihar.

Ya kara da cewa, “Za mu ci gaba da kai samame don tabbatar da cewa Kano ta kasance cikin aminci da zama lafiya.”