’Yan sanda sun tsare malamai uku da suka jagoranci sallar idi da ta Juma’a a garin Zaria jihar Kaduna.
Yanzu kwana hudu ke nan babu bayani game da daya daga cikin malaman wanda ke tsare a Sashen Binciken Mayan Laifuka na rundunar ‘yan sanda (CID).
Biyu daga cikin malaman sun amsa tambayoyi ne kan Idin karamar salla da suka jagoranta a ranakun Asabar 23 da Lahadi 24 ga watan Mayu.
– Sallar Idi ranar Asabar
’Yan sanda sun gayyaci Sheik Sani Khalifa tare da yi masa tambayoyi ne kan sallar Idi da ya yi limanci a ranar Asabar. Daga bisani jami’an ‘yan sandan sun sake shi.
Malamin jagoranci sallar ne bayan jagoran Darikar Tijjaniya na Najeriya Sheikh Dahiru Bauchi ya ayyana Asabar 23 ga watan Mayu da matsayin 1 ga watan Shawwal 1441 Hijiriyya.
– Sallar Idin ranar Lahadi
A ranar Lahadi kuma jami’an ‘yan sanda sun tsare Sardauna Limamin Bizara wanda a ranar ya jagoranci sallar Idi a kauyen da ke hanyar Zaria zuwa Jos.
Daga baya shi ma ‘yan sandan sun rabu da shi.
– Sallar Juma’a a karamin masallaci
Tun a ranar Juma’a ne ‘yan sanda suka fara tsare wani Malam Muhammad Tukur Idris da ya yi limancin sallar Juma’a a wani karamin masallaci a kan layin Agoro-Gaskiya a garin Zaria.
Zuwa ranar Talata malamin na tsare a sashen binciken manyan laifuka (CID) da ke hedkwatar Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar Izala (JIBWIS) reshen Zaria, Sheik Sani Yakubu ya tabbatar wa wakilinmu cewa duk kokarinsu na samun belin malam ya faskara.
Wakilinmu ya nemi sanin halin da malamin ke ciki ta hannun kakarin rundunar ‘yan sandan Muhammad Jalige, wanda ya ce zai bincika ya tuntubi wakilin namu.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, babu wani bayani daga bakin kakakin rundunar ba.