Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta sami nasarar kama wani mutum mai suna Bitrus Gyan wanda take zargin ya daɗe yana yi wa ’yan bindiga safarar bindigogi.
Kakakin rundunar ASP Mansur Hassan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a yammacin ranar Juma’a.
- ‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu
- A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu
Ya bayyana cewa an kama Bitrus Gyan ne a hanyar Buruku zuwa Birnin Gwari a lokacin da jami’ansu da ke yankin ke gudanar da sintiri a kan hayar.
ASP Hassan, ya ce bayan da aka tsayar da shi ne ana binciken motarsa ƙirar Golf mai launin baƙi sai aka sami bindigogi AK47 ƙirar gida guda 20 da kuma ƙwanson harsasai.
Bitrus Gyan wanda ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi ne ta Jihar Filato ya bayyana wa ’yan sandan cewa ba wannan ne karon farko da yake wucewa da makamai ba.
Kakakin Rundunar ya ce, kawo yanzu wadda ake zargin yana ba jami’ansu haɗin kai da muhimman bayanai domin kamo waɗanda yake kai wa makaman.
Kwamishinan ’yan sandan Kaduna, Audu Ali Dabigi ya jinjina wa jami’an bisa namijin ƙoƙarin da suka yi.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Kaduna cewa sai sun ga bayan miyagu da ke hana su barci a faɗin jihar.