Rundunar ’Yan sandn Jihar Kano a karkashin shirinta na ‘Shege-ka-fasa’da ke yaki da ’yan fashi da suke fakewa da daba ta kama wani da ake zargi kasurgumin dan daba ne da ya dade yana cutar da mutanen jihar.
Wanda ake zargin mai suna Isyaku Auwalu da aka fi sani da Yakuwa, Kakakin Rundunar DSP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa Yakuwa da yaransa sun dade suna addabar jama’a ta hanyar amfani da makaman gargajiya da suka hada da adduna da wukake da sanduna da takubbi da sauransu, inda suke kwace wa mutane wayoyi da kudi da sauran abubuwa masu daraja a Unguwar Yakasai da kofar Nasarawa da Kasuwar Rimi.
DSP Majiya ya ce baya ga kwace da Isyaku Yakuwa ke yi “A wasu lokuta an sha kama shi bisa zargin kashe mutane da ji musu raunuka, domin ko a ranar ya yi wa wani jami’in sintiri a rauni. Rundunarmu ta yi yunkurin kama shi lokacin da ya aikata wani laifi na kisan kai amma sai a ya gudu daga jihar. Sai yanzu Allah Ya ba mu sa’ar kama shi,” inji Majiya.
Ya ce Yakuwa da wani abokinsa mai suna Umar wanda aka fi sani da Chiwa suna hannun ’yan sanda suna bincike a kansu.