’Yan sanda sun cafke dan takarar Sanatan Borno ta Tsakiya a majalisar Dattijai na jam’iyyar NNPP, Hon Attom Muhammad Maigira, sannan an kulle ofishin jam’iyyar da ke Maiduguri.
Hukumar Raya Birane ta Jihar ta Borno ce dai ta rufe ofishin jam’iyyar ranar Alhamis.
- Mutum 9 sun kamu da Kyandar Biri a Abiya
- Shugaban ’yan sandan Japan ya yi murabus kan kashe tsohon Fira Minista
Dan takarar Gwamnan jihar a jam’iyyar ta NNPP, Dokta Umaru Alkali ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a Maiduguri.
Ya kuma ce an kama dan takarar Sanatan nasu ne bayan ya ki amsa gayyatar da ’yan sandan suka yi masa, kuma yanzu yana tsare a hannunsu.
Umaru Alkali ya ce an kuma jibge tarin jami’an tsaro a sakatariyar jam’iyyar da ke kan titin Abbaganaram da Gidan Madara tsakanin Laraba zuwa Alhamis don hana ’yan jam’iyyar shiga cikinta.
Da wakilinmu ya ziyarci sakatariyar da misalin karfe 11:30 na safe, ya iske ’yan sanda da jami’an tsaron rundunar CJTF da motocin sintiri a wajen.
Majiyarmu ta ce a ranar Larabar da ta gabata ne dai rikici ya barke a cikin sakatariyar, inda shugabannin jam’iyyar suka dauki hayar wasu leburori da za su yi wa sabuwar sakatariyar fenti gabanin ziyarar da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso zai kai a kwanaki masu zuwa.
Kwankwaso zai kai ziyarar ce domin kaddamar da sakatariyar, jam’iyyar.
Sai dai bayan kammala aikin, wasu ’yan dabar da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka mamaye sakatariyar tare da lika fastoci ’yan takararsu a wurare masu mahimmanci a cikin harabar sabuwar sakatariyar.
Hakan dai bai yiwa magoya bayan NNPP dadi ba wanda ya kai ga fada.
Wata majiyar kuma ta ce, sakatariyar NNPP tana wani yanki ne a cikin babban birnin, lamarin da ya sa jami’an hukumar raya birane na Jihar ta Borno suka rufe ta bayan sun aika musu sako amma suka yi mursisi suka ki biyayya.
Shugabannin jam’iyyar dai na zargin hannun jam’iyyar APC mai mulki da shirya kitimurmurar da ta kai ga rikicin don ta samu ta rufe hedkwatar.
Sai dai a wani martani da ya mayar, shugaban jam’iyyar APC mai mulki a jihar, Ali Bukar Dalori, ya yi watsi da zarge-zargen.
“Ina so in sanar da ku cewa, APC a Borno ba ta da alaka da rufe sakatariyar NNPP kamar yadda Hon Attom ya yi zargin.”
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Borno, DSP Sani Sha-Tambaya, ya ce bai san da faruwar lamarin ba.