✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama daliban Zakzaky 78 a Kaduna – IMN

Kungiyar ta ce an kama mutanen ne a Kaduna da Zariya lokacin muzahara

Kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN) da ke karkashin shugabancin Sheikh Ibrahim EL-Zakzaky ta zargi ’yan sanda da kama kama mata mambobi 78 a Jihar Kaduna.

IMN ta ce an kama mutanen ne lokacin muzaharar Ranar Quds a Zariya da
kuma cikin garin Kaduna.

A cewar kungiyar, akalla ’ya’yanta 70 ne aka kama a Zariya a yayin da kuma takwas aka kama su a tsakiyar garin Kaduna a lokacin muzahar da suka yi a ranar Juma’a, 29 ga watan Afrilu, 2022.

Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna, daya daga cikin shugabannin
kungiyar, Injiniya Yunusa Lawal Musa, ya yi zargin cewa ’yan sanda sun kuma harbe daya daga cikin ’ya’yan kungiyar mai suna Mustafa Abubakar Wagini.

Ya ce a yanzu haka, wadanda ke tsare su 78 ne a hedikwatar ’yan sandan Jihar.

“Mun tabbatar da kama mutum 70 a Zariya sannan takwas a garin Kaduna.
wanda a yanzu haka an kawo wadanda aka kama a Zariya suna hedkwatar
’yan sandan Jihar.

“Sannan an kashe mana mutum daya mai shekara 28 da haihuwa mai suna Mustafa Abubakar Wagini.

“Wannan muzahara da aka yi a wannan rana duk duniya aka yi ta ciki har da Amurka da Ingila da Jamus da Faransa da sauran kasashe, kuma babu inda aka kai masu hari sai a Najeriya. Mun yi Allah wadai da wannan hari na ’yan sanda domin kuwa dokar kasar nan ta ba mu yancin gudanar da addininmu kamar kowa,”inji shi.

Ya kara da cewa lauyoyinsu na nan na kokarin yadda za su fito da mutanen da ke tsare, sai dai ya yi kira ga ’yan Najeria da su yi kira ga gwamnatin ta sakar wa Shugaban kungiyar, Sheikh Zakzaky fasfo din shi da na matarsa, Zeenatu Zakzaky.

Kokarin jin ta bakin kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed ya ci tura saboda bai amsa wayarsa ba har ya zuwa lokacin hada wannan labari.