✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama bindigogin AK-47 a Kano

’Yan sanda sun kama bindigogi kirar AK-47 guda hudu da ake kokarin yin fasakwaurinsu zuwa Kano.

’Yan sanda sun kama bindigogi kirar AK-47 guda hudu da ake kokarin yin fasakwaurinsu zuwa Jihar Kano.

A ranar Juma’a ne ’yan sanda da ke sintiri a Kwanar Garko da ke kan hanyar Bauchi zuwa Kano suka gano bindigogin a cikin wata bas kirar Hiace.

Masu motar na hango ’yan sanda, sai motar ta fara kokarin juyawa, inda daya daga cikin mutanen motar ya fito ya jefar da kunshin wani abu a cikin buhu, suka ja motar suka tsere.

Daga baya da ’yans sanda suka duba sai suka gano bindigogi kirar AK-47 guda hudu a ciki.

Da yake sanar da hakan, kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce rundunarsu tana ci gaba da bincike domin kamo mutanen da suka tsere.

A cewarsa, Mukkaddashin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, DCP Mu’azu U. Mohammed, ya jinjina wa mutanen jihar kan hadin kan da suke ba wa rundunar.

Ya kuma bukace su da su kai rahoton duk wani wanda ba su aminta da motsinsa ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.