✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama akuyar da ta jawo cinkoson motoci

Sun kama akuyar ba tare da wata matsala ba.

’Yan sandan Birtaniya sun kama wata akuya da ta kwace daga masu ita inda ta jawo “cinkoson a garin Lancaster kamar yadda kafar labarai ta UPI ta ruwaito.

’Yan sandan Lancaster sun tabbatar a shafinsu na Facebook cewa sun kama akuyar ba tare da wata matsala ba bayan sun yi ta guje-gujen kama ta a tsakanin abubuwan hawa.

Akuyar wadda ake kira da Houdini, an kama ta ce a Titin Wyresdale kusa da wurin shakatawa na Williamson Park, inda ake gudanar da wani gagarumin biki na Highest Point kamar yadda rediyon Beyong na North Lancashire ya bayyana.

’Yan sandan sun ce “Bayan dogon lokaci ana guje-guje daga BOWERHAM zuwa WYRESDALE RD, tare da jawo cinkoson ababe hawa, muna farin cikin sanar da ku mun kama akuyar da kubuce wadda muka sanya mata suna Houdini!”

Sun yaba wa masu aikin ceton dabbobin gida na Wolfwood kan gudunmawar da suka bayar wajen ceto akuyar tare da mika godiya ga Kamfanin Ashton kan daukar akuyar a mota zuwa inda za a ajiye ta.

A makon jiya ma a cikin garin Chatham Township, N.J, an ga ’yan sanda suna neman wata “akuya da ke leken gidan mutane.”

An ga akuyar tana karakaina a garin tana lelleka gidan mutane kafin a kama ta.