✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ƙwato motoci 13 a hannun ’yan fashi a Abuja

An dai ƙwato motoci 13 daga hannun waɗanda ake zargin da sauran kayayyakin da aka gano kamar na’urorin cire kuɗi na POS da kwamfutocin lapton.

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wasu mutane bakwai da ake zargin ’yan fashi da makami ne tare da ƙwato motoci 13.

Kwamishinan ‘Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu wanda ya gabatar da waɗanda ake zargin a ranar Alhamis, ya ce an kama su ne ta hanyar tattara bayanan sirri tare da sa ido da kuma kai samame.

Ya ce, waɗanda aka kama suna da alaƙa da wani gungu dawani mai suna Friday Ogwuche ke jagoranta, inda suke gudanar da ayyukansu a tsakanin yankunan Mararaba a Jihar Nasarawa da Abuja.

CP Olatunji ya ce uku daga cikin waɗanda ake zargin sun haɗa da Godwin Abba ɗan jihar Benuwe da Abraham Anthony daga jihar Kaduna da kuma Moses Obi daga jihar Cross River duk sun taka rawa wajen lalubo waɗanda ba a san ko su wanene ba a unguwar Mararaba, da yankunan AYA junction da yankunan Kubwa.

A cewarsa, waɗanda ake zargin sun fi kai wa waɗanda harin ya rutsa da su ne a lokacin da masu tafiya aiyuka da safiya ke cunkoson jama’a da kuma wuraren tashar motoci da kasuwar Nyanya.

“Sakamakon nasarar kama ɓarayin da aka yi ya kai ga kama wasu mutane uku da ake zargi da ƙwarewa wajen yi wa fasinjoji sata ta ɓarauniyar hanya,” in ji shi.

Kwamishinan, wanda ya kuma bayyana sunayen sauran mutanen ukun da: Stephen Moses, ɗan asalin jihar Benuwe, Jude Simon, da kuma Terfa Akaaer, shi ma daga jihar Benuwe, ya ce Tarfa da ke zaune kusa da wurin shaƙatawa na Mararaba, na haɗa kai da rukunin ɓarayin wajen kai hari ga waɗanda abin ya shafa.

Ya kuma bayyana cewa an ƙwato motoci 13 daga hannun waɗanda ake zargin ke amfani da su, inda ya ƙara da cewa, sauran kayayyakin da aka gano sun haɗa da na’urorin cire kuɗi ta POS guda uku, kwamfutocin tafi-da-gidanka 5 (laptop), wayoyin salula uku, dalar Amurka 203, katin ma’adanar waya 109, da kuma filala.

Ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.