✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Sanda sun kai samame makarantar Islamiyya sun kwashe dalibai 300 a Kaduna

A cewar rundunar ‘yan sandan takai samamen ne bayan ta samu labarin cewa, ana cin zarafin daliban makarantar mai suna Ahmad Bn Hambal wacce take…

A cewar rundunar ‘yan sandan takai samamen ne bayan ta samu labarin cewa, ana cin zarafin daliban makarantar mai suna Ahmad Bn Hambal wacce take layin mai dubun tsumma a Rigasa Karamar Hukumar Igabi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce ko da suka kai samamen sun tarar da wasu daliban a daure cikin mari.

“Wasu daga cikinsu kuma akwai tabon rauni a bayansu wanda hakan ke nuna cewa ana cin zarafinsu a wannan makaranta da sunan koya masu karatun alkur’ani. Dan haka muna ci gaba da bincike domin gano mai makarantar,” in ji shi.

Ya kuma tabbatar da cewa, rundunar zata mikawa iyayen yaransu da zarar an mika su ga gwamnatin jihar.

Sai dai Aminiya ta samu zantawa da daya daga cikin mazauna unguwar kuma wanda yake zuwa wa’azi a makarantar mai suna Malam Shehu wanda ya karyata wannan zargi na ‘yan sanda.

“Ni ina daya daga ckin masu zuwa wa’azi a makarantar kuma iyayen yaran su suka kawo ‘ya’yansu kangararru zuwa makarantar domin a kula masu da su. Baya ga haka babu abin da ake karantar da su illa kur’ani saboda haka ba gaskiya ba ne a ce wai ana cin zarafin yara a makarantar.

Daya daga cikin daliban

“Koda ‘Yan Sandan suka zo, bayan sun tafi iyayen yaran da suka kwashe ai sun zo makarantar da nufin ganin ‘ya’yansu. Kuma ai akwai iyayen da ke kawo wa ‘ya’yansu abinci a kullum wanda da ana cin zarafin yaran nasu ai zasu yi magana.” In ji shi.