A yau Juma’a ne ‘yan sanda suka kai samame gidan Sanata Dino Melaye da ke unguwar Maitama a Abuja da nufin kama shi.
‘Yan sandan sun isa gidan Sanatan da motoci biyar da misalin karfe 12:30 na rana. ‘Yan sandan sun yi amfani da motoci biyu wajen rufe kofar shiga gidan Sanatan yayin da wasu kuma ‘yan sandan suka tsaya a kofar gidan.
Wani daga cikin ‘yan sanda cikin fafin kaya ya bayyana wa manema labarai cewa, sun gidan ne da nufin tsare Sanatan, sauran karin bayanin su tuntubi kakakin hukumar ‘yan sandan Najeriya Jimoh Moshood.