✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun harbe ’yan fashi, sun cafke wasu 8

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Akwa Ibom ta ce jami’anta sun harbe ’yan fashi biyu suka kuma kama wasu ’yan fashin guda takwas. Kakakin rundunar,…

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Akwa Ibom ta ce jami’anta sun harbe ’yan fashi biyu suka kuma kama wasu ’yan fashin guda takwas.

Kakakin rundunar, SP Odiko Macdon ya ce, jami’an sun bindige biyu daga cikin ’yan fashin sannan suka harbi wasu uku a Obo Annang, Karamar Hukumar Essien Udim.

Ya ce an kama ’yan fashin da kananan bindigogi biyu kirar gida, harsashi 86, layu, layukan waya, tsabar kudi, da sauransu.

Wata takarda da ke yawo a jihar, dauke da sa hannun kakakin rundunar ta cafke wasu gungun masu laifi su biyar da ake zargi da yin fashi a Kasuwar Obo Annang a Karamar Hukumar Essien Udim.

“Ranar 25 ga Nuwamba 2020, mun samu rahoton kama ’yan fashi a yayin da suke tsaka da gudanar da fashin a shataletalen Obo Annang a Karamar Hukumar Essien Udim.

Rundunar ta yi kira ga jama’ar jihar da su sanya idanu a kan duk wani abu da ba su gane ba, ko yake musu barazana ta fuskar zaman lafiyarsu.

Macdon ya ce, rundunar a shirye take wurin tabbatar da kare lafiya da dukiyar al’umar jihar.