’Yan sanda sun bindige wani babiyin akidar Shi’a, suka kuma jikkata wasu da dama a wata arangama da aka yi a tsakaninsu a Abuja.
Duruwan ’yan Shi’a karkashin Haraka Islamiyya (IMN), sun yi karon batta ne da ’yan sanda a yayin da suke tattakin zagayowar ranar jagoransu a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, wanda ke tsare a hannun gwamanti.
Wani daga cikin masu tattakin mai suna Yahaya Soje, ya ce bayan mutumin da aka kashe din, an garzaya da wadanda suka samu rauni daga cikinsu zuwa asibiti domin samun kulawa.
Ya ce sun fara tattakin ne daga ofishin Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa da ke unguwar Maitama, inda a hanya suka gamu da jami’an ’yan sanda da suka buda musu wuta.
Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja ta ce masu tattakin na ranar Litinin sun tayar da tarzoma ne, inda suka rika lalata kayan gwamnati, suna kai wa mutane farmaki, da jifar ’yan sanda da duwatsu da wasu muggan abubawa.