Rundunar ’yan sanda ta jihar Borno ta ce ba za ta lamunci kowace irin zanga-zanga da za ta kawo tarnaki ga zaman lafiyan da ake kokarin samu a jihar ba.
Kakakin rundunar a jihar, DSP Edet Okon ta ba da sanarwar a Maiduguri ranar Talata.
Ta ce bayanai na nunid a cewa wasu bata-gari na neman yin amfani da karin farashin wutar lantarki, man fetur da halin da ma’aikatan jihar ke ciki su yi zanga-zanga.
A cewar sanarwar, “Kwamishinan ’yan sandan Jihar Borno, CP Mohammed Ndatsu Aliyu na sanar da jama’a cewa ba za mu lamunci yunkurin na yin zagon kasa ga ayyukan gwamnati da jami’an tsaro na wanzar da zaman lafiya ba.
“Rundunarmu na amfani da wannan damar ta tunatar da al’umma cewa dokar hana kowane irin gangami na nan daram.
“Muna bayar da shawara a mika kowane irin korafi a inda ya dace.
“Yana da kyau a lura cewa gamayyara kungiyar kwadago a jihar a sanarwarta ta ranar 7 ga Satumba ta nesanta kanta da kowane irin zanga-zanga a jihar”, inji DSP Edet.
Ya ce saboda rundunar za ta dauki kowane yinkuri na zanga-zanga a matsayin zagon kasa ga tsarin zaman lafiya a jihar ta Borno.
“Daga wannan sanarwar, muna shawartar duk wani mai kokarin yin zanga-zanga a fadin Jihar Borno da ya girmama doka ta hanyar kiyayewa”, inji sanarwar.