✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja

Rundunar ta ƙwato makamai ciki har da bindiga AK-49.

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga, Salisu Mohammed, wanda aka fi sani da Dogo Saleh, a wani artabu da suka yi da shi a dajin Gidan-Abe da ke kan iyakar Bwari da Kaduna.

Sun samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri kan shigowar ‘yan bindiga yankin daga Kaduna.

Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Olatunji Rilwan Disu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce jami’an rundunar yaƙi da garkuwa da mutane, ƙarƙashin jagorancin Mustapha Muhammed, sun tare hanyar ’yan bindigar, inda suka yi musayar wuta da su.

“Mun yi nasarar kawar da barazana babba da ke addabar al’umma da hanyoyi,” in ji Disu.

An gano cewa Mohammed, mai shekaru 21, yana ɗaya daga cikin manyan ’yan bindigar da ke aiki a dajin Rijana na Kaduna.

“Ya sace mutane da yawa, ciki har da kashe jami’an tsaro da fararen hula.

“Jami’an tsaro sun ƙwato bindiga ƙirar AK-49, harsasai 60, da kuma Naira miliyan uku, da ake zargin kuɗin fansa ne da suka samu daga garkuwa da mutane,” in ji shi.

Bincike ya tabbatar da cewa ɗan bindigar na da hannu a kai hare-hare kauyukan Kike da Bagada, inda ya jagoranci garkuwa da mutane tare da karɓar kuɗin fansa.

“Ayyukansa sun jefa jama’a cikin fargaba, amma jami’anmu sun aika da saƙo mai ƙarfi cewa ba za a lamunci aikata laifi ba,” in ji Disu.

Wani jami’in ’yan sanda ya samu rauni kaɗan a yayin artabun, amma an ba shi kulawar da ya dace, inda yake murmurewa.

A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da farautar sauran ‘yan bindigar da suka tsere tare da rushe duk wani sansanin ’yan bindiga da ke iyakar Abuja da Kaduna.