Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, shiya ta biyar, Mista Sholla David ya gargadi masu tayar da zaune tsaye da suna zanga-zangar #EndSARS da su bar titunan jihohin Delta da Edo.
Ya kuma tabbatarwa da matasan jihohin cewar hukumar ‘yan sandan a shirye ta ke ta gudanar da aikinta kamar yadda tsarin mulkin kasa ya zayyana.
Ba mu da ikon hukunta babban sufeton ’yan sanda – Hukumar ’yan sanda
#EndSARS: ‘Yan sanda sun hana matasa dibar abincin tallafi
#EndSARS: An kona ofisoshin ‘yan sanda 2 da na AIT a Edo
Shalla ya kuma shawarci iyaye kan su gargadi ‘yayansu da su kaucewa aikata miyagun laifuka ko shiga cikin masu tayar da tarzoma ko kisan kai ko sata da salwantar da dukiyoyin gwamnati da na al’umma.
A nashi jawabin, kwamishinan ‘yansanda na jihar Edo, Babatunde Johnson Kokumo, ya ce sun kama ‘yan daba da dama bayan zanga-zanga a jihar.
Ya ce fasa rumbunan da aka yi ranar Asabar manuniya ce kan yadda masu zanga-zangar suka rikide zuwa ‘yan daba da masu kone-kone, kuma duk wanda aka kama zai yabawa aya zakinta.
Aminiya ta gano cewa sakamakon kone-konen da ake yi, Sojoji da ‘Yan sanda sun fara tsaron kaddarorin gwamnati a Edo don kawo karshen kai musu hari a jihar.
Ana alakanta matakin jami’an tsaron da barazanar da wani mutum ya yi na kai hari bangarorin gwamnati da dama a jihar.