✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga a Zamfara

An yu artabu da jami'an tsaro da 'yan bindigar.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta sanar da dakile harin ‘yan bindiga a wasu kauyukan masarautar Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru a jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce an kwato wasu makamai daga hannun ‘yan bindigar a lokacin da suka yi yunkurin kai harin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya fitar a ranar Laraba a Gusau.

A cewar Shehu, daga ranar 11 ga watan Nuwamba zuwa 14 ga watan Nuwamba, an tura ‘yan sanda zuwa wasu wuraren da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga a Masarautar Dansadau.

“Da zuwan jami’an suka mayar da martani ba tare da bata lokaci ba.

“An yi kazamin artabu tsakanin ‘yan bindiga da jami’an, wanda ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa zuwa cikin daji.”

Ya bayyana cewa an kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu tare da alburusai 35.

Shehu ya kuma ce rundunar ta kama wasu mutane 16 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da fashi  da makami, sata, garkuwa da mutane, da kuma kisan kai.

“Sabbin dabarun yaki da miyagun laifuka na rundunar tana samar da sakamako mai kyau saboda a halin yanzu tana dakile matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar.

“An kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane da kuma aikata sata a wasu sassan kananan hukumomin Bukkuyum da Gusau.

“Rundunar ta kuma yi nasarar cafke ’yan fashin a garin Kwatarkwashi na Karamar Hukumar Bungudu.”

Kakakin ya ce an kuma kama wani da ake zargin dan fashi ne, wanda ya shahara wajen ta’addanci a kauyukan Karamar Hukumar Tsafe da wajen Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce rundunar ‘yan sandan hadin gwiwa da ‘yan banga sun kama wani da ake zargi da aikata laifin a hanyar Anka zuwa Bukkuyum.

%d bloggers like this: