Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta dakile wani farmaki da wasu ’yan fashi suka kai a jihar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Bola Longe ne ya bayyana hakan.
- ‘Tsoron sake sanya dokar kulle ne ya sa muka shiga fashi da makami’
- ’Yan fashi sun harbe mai yi wa kasa hidima
- ‘Yunwa ce ta sa mu yin fashi da makami’
Ya ce sun samu kira, inda aka sanar da su cewa bata-gari da ake zaton ’yan fashi ne sun tare titin Gidan Gambo, da ke kan hanyar Lafia-Shendam.
Ya kara da cewa daga nan aka aike da jami’an ’yan sandan yankin Assakio, inda suka yi musayar wutar da ’yan fashin.
A yayin dauki ba dadin, ’yan sandan sun yi nasarar kashe daya daga cikin ’yan fashin wanda aka garzaya da shi asibiti, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Longe, ya ce an kwace adduna, wukake, da sauran makamai a hannun ’yan fashin, yayin da ragowar tsere cikin daji da raunuka.
A cewarsa jami’an ‘yan sandan na ci gaba da sintiri a dajin domin gano maboyar ragowar da suka tsere.
Kwamishinan ’yan sandan ya gargadi masu aikata laifuka a jihar da su guji fadawa hannun rundunar, domin ba za ta raga musu ba.